1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahamadou Issoufou na neman taka wa Hama Amadou birki

Salissou Boukari AH
August 14, 2019

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya nemi shugaban Kasar Benin da ya tiso keyar Hama Amadou zuwa gida, wannan tsokaci ya janyo muhawara a kasar.

https://p.dw.com/p/3NuEV
Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Hoto: AFP/I Sanogo

A Jamhuriyar Nijar wata hira da Shugaban Kasar Issoufou Mahamdou ya yi da wata jarida ta haifar da muhawara musamman ma inda kusan a karon farko ya yi magana kan babban mai adawa da shi Hama Amadou. Wanda a halin yanzu yake gudun hijira a Jamhuriyar Benin mai makwabtaka da Nijar. A tattaunawar da aka yi da shi, ya jaddada matsayinsa na neman a taso masa keyar Hama Amadou zuwa Nijar ko kuma a nesantar da shi daga kasar ta Benin. Lamarin da ake ganin tamkar babu wata alama ta yin sulhu tsakanin wadanda a baya suka kasance abokan juna.