Nijar: Shirin zaben gama-gari | Siyasa | DW | 21.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Shirin zaben gama-gari

Bayan tabbatar da jerin sunayan 'yan takarar shugabancin kasa a Jamhuiriyar Nijar, hukumar zaben kasar CENI ta sanar da soma rarraba katunan zabe a fadin kasar.

A ranar 21 ga watan Febrairu na 2016 ne za a gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a Jamhuriyar Nijar, wanda kotun tsarin mulkin kasar ta amince da takardun 'yan takara 15 daga cikin 16 da aka gabatar a gabanta. Hakan ya nunar cewa 'yan takara 15 ne za su fafata a zaben na shugaban kasa. Sai dai kuma daya daga cikinsu Hama Amadou na jam'iyyar Moden FA Lumana Afrika, na ci gaba da zama a gidan yari na garin Fillingue da ke a nisan kilomita kusan 200 da Yamai babban birnin kasar.

DW.COM