Nijar: Shawarwari kan kasafin kudi na 2018 | Siyasa | DW | 16.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Shawarwari kan kasafin kudi na 2018

Kungiyoyin fararen hula masu yakar sabon kasafin kudi a Nijar sun baiwa majalisar dokokin kasar cikakkun shawarwari da ma hanyoyin suka dace gwamnati ta bi don samun kudaden shiga baya ga batu na karbar haraji.

Malam Moussa Tchangari daya daga cikin 'yan gwagwarmayar na kungiyoyin fararen hula masu fatan kawo sauyi ga sabon kasafin kudin na kasa ya karanto wasu jerin matsalolin da suka lura sabon kasafin na sabuwar shekarar ya kunsa da kuma gwamnatin ta Nijar ta gabatar da shi a gaban majalisa kana ta ke jiran majalisar dokoki ta lamunce mata domin ya kasance doka.

A ranar 13 ga wannan watan majalisar dokoki ta kasa ta saurari ra'ayoyin 'yan fararen hular tare da tattauanawa da su a wani yunkurin na majalisar na shimfida fahimtar juna tsakanin bangarorin kolin kasar da 'yan fararen hular da yau sama da makwanni biyar kenan suke ta famar tayar da kayar baya game da sabon kasafin. Malam Mamane Nouri wanda kusa ne a kungiyoyin ADDC wadata kuma mamba a jerin kungiyoyin na fararen hula ya ce ''mun gana da su kuma su kansu suka ce sun gamsu da shwarwarin da muka basu.''

Kungiyoyin dai na zargin gwamnatin ne da son amfani da wasu hanyoyi na daban ta hanyar haraji don matso tattalin arziki daga jama'a a cikin sabon kasafin don saka mafi yawan kudaden da ta tatso zuwa ga wasu fannoni na jin dadin gwamnati kawai a yayin da kasafin bai wuce kashi 11.99% na fannin ilimi ba a ya yin da fannin noma da kiyo ko wannensu bai wuce kaso 6% ba. A cewar Malam Ali Idrissa na kungiyoyin Rotab bukatar su ita ce gwamnatin ta sake salo inda ya kara da cewar ''ya kamata a rage kashe kudaden gwamanti, bai kamata ba a ce kasa kamar Nijar ana da minista fiye da 40.''

 

Sauti da bidiyo akan labarin