Nijar: Sabuwar gwamnati ta kama aiki | Zamantakewa | DW | 08.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Nijar: Sabuwar gwamnati ta kama aiki

Sabon shugaban kasar Nijar Malam Bazoum Mohammed ya ci alwashin gudanar da ayyukan raya kasa domin ciyar da kasar gaba.

Tun bayn shan rantsuwar kama aiki sabon shugaban kasar Nijar Malam Bazoum Mohammed ya ci alwashin aiki tukuru domin ciyar da kasar gaba.

A ranar Juma'ar da ta gabata ma sai da shugaban ya lashi takobin yaki da masu da'awar jihadi wadanda ke kai hare haren babu gaira babu dalili inda suke fararen da basu ji ba basu gani ba yana mai cewa wannan laifukan yaki ne suka aikata.

Tuni dai shugaban ya nada sabon Firaminista Ouhoumoudou Mahamadou da Ministoci 33 da suka hada da mata shidda.

 

 


 

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin