Nijar: Rikicin magoya bayan Bazoum da na Issoufou
January 15, 2026
A 'yan kwanakin baya bayan nan wani sabon sabani ne ke tasowa a kafofin sada zumunta na zamani tsakanin magoya bayan Mohamed Bazoum da sojojin suka hambarar da kuma masu goyon bayan tsohon shugaban kasar Issoufou Mahamadou da suke nunawa juna yatsa dangane da cin amana yayin da wasu ke zargin hada baki da sojojin kasar wajen kifar da gwamnatin.
To sai dai ga Alhaji Jafar Abdou Dubai daga cikin masu goyon bayan tsohon shugaban kasar Issoufou Mahamadou ya ce idan za a yi maganar cin amana to kamata yayi a yi wiwaye adon tafiya.
A wannan sabon rikicin da ke zaman irin shi na biyu tun bayan juyin milkin zarge zarge ne ke tasowa to amman ga Sahanun Mahaman lamarin ya wuce zargi domin sun tattara hujjoji.
A yanayin da ake ciki dai yanzu a kasar, babu wata jam'iya mai magana da yawun siyasa bayan da sojojin suka soke su. Daman dai tun a gabanin siyasa wannan alakar ta dauko asalin ne a wata kungiyar abokantaka da suka yi sama da shekaru 30 a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Issoufou Mahamadou kamun su mayar da ita jam'iyar siyasa