SiyasaAfirka
An rasa rayuka a hatsarin kamfanin COMINAK a Nijar
January 17, 2022Talla
Mutane biyu sun halaka a yayin da wasu karin mutum biyun suka ji munanan raunuka a wata rugujewar kayan aiki da ta faru a kamfanin COMINAK da ke sarrafa makamashin nikiliya na Uranium a Jamhuriyar Nijar.
Hukumomin kamfanin mallakin kasar Faransa ne suka sanar da haka a yammacin ranar Lahadi.