Nijar: Mutane 16 na neman kujerar shugaban kasa | Siyasa | DW | 04.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Mutane 16 na neman kujerar shugaban kasa

An kammala karbar sunayen wanda za su yi takarar kujerar shugaban kasa a Nijar inda yanzu haka ake da mutane 16 da ke neman wannan mukami.

'Yan takara 15 ne dai za su fafata da shugaba Muhamadou Issufou da yanzu haka ke jagorantar kasar karakshin inuwar jam'iyyar PNDS Tarayya. Daga cikin wadannan muatne dai akwai Seini Oumar na jam'iyyar MNSD Nasara wadda ke zaman jagora ta jam'iyyun adawa a Nijar din da kuma Hama Amadou tsohon kakakin majalisar dokoki wanda zai yi wa jam'iyyarsa ta Moden Lumana Afrika takara.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou

Shugaba Muhamadou Issufou zai yi takara da mutane 15 daga jam'iyyu daban-daban.

Sauran mutanen sun hada da Mahaman Ousmane tsohon shugaban kasa wanda jam'iyyar MNRD Hakuri ta tsaida a matsayin dan takarar ta kana akwai Ibrahim Yakouba na jaririyar jam'iyar nan da ake kira MPN Kishin Kasa wanda ta samu karbuwa wajen matasa. Baya ga wadannan, akwai sauran 'yan takara da ake ganin za su yi tasiri a kakar zaben na wannan karon, wanda ake sa ran yin sa ranar 21 ga watan Fabrairun da ke tafe.

Ranar Asabar da ta gaba ne aka rufe karbar takardun 'yan takara, kuma yanzu haka abin da ya rage shi ne jami'an tsaro na kasar su gudanar da bincike kafin daga bisani kotun koli ta aiwatar da na ta bincike kana ta yanke hukunci a kai. Tuni dai 'yan takara a zaben suka fara bayyana irin abubuwan da suke son aiwatar da zarar 'yan kasar sun basu dama ciki kuwa har da batun cin hanci da rashin adalaci da ake yi wa talakawa da makamantan wannan.

Hama Amadou

Hama Amadou na daga cikin 'yan takara na adawa da ke kan gaba a fafutukar neman kujerar shugaban kasa.

Dama dai kungiyoyi na fararen hula sun jima suna sukar gwamnati da 'yan siyasar kasar wajen yi wa talakawan da su ka zabesu adalci yayin jagoracin da suke yi. Diori Ibrahim jami'in babbar kungiyar da ta hada kungiyoyin farar hulan Nijar din wato Alternative Espace Citoyen ya ce'''ya kamata 'yan siyasa su ji tausayin kasar da talakawanta''.

Sauti da bidiyo akan labarin