1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Minista Ben Omar ya rasu

Mahaman Kanta AMA
May 3, 2020

Allah ya yi wa daya daga cikin ministocin Jamhuriyar Nijar Malam Ben Omar Mohamed rasuwa a wani babban asibitin birnin Yamai a Lahadin nan, bayan 'yar gajeriyar jinya.

https://p.dw.com/p/3biii
Niger Flagge

Duk da yake kawo yanzu ba a kai ga tabbatar da dalilan mutuwarsa ba, wakilin DW Hausa a birnin Niamey Mahaman Kanta ya tabbatar da rasuwar Ben Omar din wanda gabannin rasuwarsa yake rike da mukamin ministan kwadagon kasar.

A wata hira da yayi da DW a kwanakin baya, Minista Ben Omar Mohamed ya bayyana matakan da gwamnatin Nijar ke  dauka wajen dakile yaduwar Corona ga ma'aikata.

Mamba a kawancen jam'iyyun da ke mulki kuma shugaban PSD Basira kana tsohon malamin jami'a, Ben Omar Mohamed ya taka muhimiyar rawa wajen tabbatar da dorewar dimukradiyar kasar.