1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Wayar da kai bisa illolin tsoffin kayan Latroni

Abdoulaye Mamane Amadou
May 30, 2018

Jamhuriyar Nijar wasu matasa ne suka tashi haikan don wayar da kan jama’a da ma fargar da su irin illolin da ke tattare da ajiyar tsoffin kayan Latroni ciki har da salula ga lafiyar jama’a da ma inganta muhalli,

https://p.dw.com/p/2ydT8
Sammelstelle für Handys
Hoto: imago/imagebroker

Matasan kan kai ga tattara tsoffin wayoyin salular da suke karba daga jama’a tare da mayar da gurbinsu da wasu ababe na amfani, inda tuni matakin ke samun karbuwa daga jama’a. Matasan kan shiga ne unguwanni ko lunguna da sakuna da ke birnin Niamey, walau a karkara don shirya taruka wa jama’a irin na wayar da kai da kan kai su ga shanyo kan dubban al’umma masu nuna dari-dari wajen amince wa da manufofinsu. Biyo bayan bayyana masu tarin matsalolin da ke tattare da tsoffin kayan latronin musamman ma na salula.

Malam Abdou Mahamane Laouali matashin injiniya ne da ke jan ragamar rukunin matasan, yace akwai wadansu batirorin telephone suna da wani sanadarai masu taba idanun jama’a, kuma a kwai yara sai kaga sun kasa tashi nan din ma wata illa ce ke tattare da wayoyi wadanda aka ba su suna wasa da su hakan kuma mata suma wasu lokuttan da akwai sinadarai da ke cikin wayoyi idan suna yawan amfani da su yakan iya kai su ga samun matsalar haifuwa.

Matashin injiniyan ya ce suna shan fuskantar rashin yarda da turjiya wasu lokuttan daga jama’a da ke nuna rashin amincewa da shawarwarin da suke bayarwa, na yin nesa-nesa da kayan su na latroni musamman wayoyi na salula da suke sababbi, ballantana ma sun tsufa. Yace ai abin mamaki ne a kira ka daga wata uwa duniya kuma kana jin mutun kasan da cewar akwai sinadarai da ke tattare da hakan saboda hakan sai kaga wani lokaci mutun ya fadi a ce ai ciwon hawan jini ne, sai kuma kaga gida daya mutun goma kowa na da wayoyi sanan abin da ka ji kasan akwai illoli. Hakan kuma yara sai a rinka basu wayoyi suna ta wasa da su ana tsamanin kayan wasa ne alhali kuwa tare suke da wasu sanadarai da ke iya lahanta yara.

Kawo yanzu daga ranar da matsan suka soma aikin na wayar da kai a bara kawo yanzu matasan sun samu nasarar tattara tsoffin salula da kayan latrnoni ga jama’a da suka haura ton kimanin 8 abubuwan da ke tabbatar da cewar sannu a hankali suna samun gagarumar nasara, kan kuma tuni bangarori daban daban na na jam’a suka fara nuna amincewar kamar yanda wasu suke bayyanawa DW.