Nijar: Martani dangane da mutanen da suka mutu a Hamada | Siyasa | DW | 16.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Martani dangane da mutanen da suka mutu a Hamada

Gawarwakin mutane 34 aka samu a Hamadar Nijar wadanda ake kyautata zato yunwa da kirshirwa suka yi sanadiyyar ajalinsu a kan hanyarsu ta zuwa ci-rani.

Niger Agadez Bild 1 Konvoi mit Migranten verlässt Agadez

Ayarin bakin haure daga Agadez a Nijar zuwa arewacin Afirka

Wannan dai shi ne hadari na biyu mafi muni a tarihin mace-maccen da ake samu a Hamadar Saharar Jamhuriyar ta Nijar sakamakon shigewar da 'yan ci-rani ke yi ta Hamadar kasar da zummar shiga kasashen arewacin Afrika ko kuwa da niyyarsu ta zuwa kasashen Turai. Babban abin da ya fi daukar hankalin kungiyoyin kare hakin mata da yara na hadarin shi ne tarin yara kankana kimanin 20 da kishirwa da yunwa suka halaka. Kungiyoyin na cigaba da cizon 'yar yatsa game da halin ko in kula da suke cewar wasu uwayen yara na yi duk ko da tsabagen tsanani na talauci da rashin walwala ta rayuwa da ke addabar jama'a.

Malama Mori Hajiya Aminata na daya daga cikin kungiyoyin da ke kare hakin mata da yara a jamhuriyar Nijar.

Ta ce: "Abu ne na bakin ciki domin duk abinda kaga zai saka mace ta fice ta bar gidanta ba wai wani kasuwanci za ta ba, a'a ta tashi ne da ciki da goyo ta je sai da rayuwa. Kowa ya san yadda al'amari yake a dajin nan na Sahara ko wadanda ke shiga teku wurin tsallakawa zuwa Turai akwai hadari, amma ka ga mace na yi shi, to ka san abu ne mai karfi."

Bincike da daukar matakai kwarara

Ko da yake hadarin bai kai ga na farkon da ya taba faruwa a cikin watan Nuwamban 2013 ba, abin da ya auku a Hamada na a matsayin abin al'ajabi ga wasu kungiyoyin da ke kare hakin yara irin su Alten.

Niger Agadez Bild 5: Straße zwischen der nigerianisch-nigrischen Grenze und Agadez

Hanya mai hatsari cikin Hamadar arewacin Nijar

A wata hira da ya yi da tashar DW shugaban kungiyar Malam Mahamadu Moussa ya ce ila tilas ne gwamnatin Nijar ta sa a gudanar da kwakkwaran bincike tare da daukar muhimman matakai kan lamarin.

Ya ce: "Gwamnati ta je ta saka a yi bincike domin binciken kirki ba wai a yi "pappap" a dawo a ce an kare ko a saka jandarma ba. Wannan ba harkar jandarma ba ce. Gobe ma idan an tare hanyar wadansu na bin wata hanya su tafi a kasa. Za a gudanar da bincike ba wai wadanda ake yi can bisa hanya ba wadanda suka mutu a dauko, wadanda aka iya kamawa aka kamo ko wadanda suke aikin baranda a watsar da su. Tushen ya kamata a bincika."

Ba shakka dai matsalar talauci da fatara da rashin aikin yi ga matasa na daga cikin wasu dalilan da ke tursasa jama'ar ficewa daga gidajensu zuwa ci-rani. A wani matakin da gwamnatin ta ce ta dauka hukumomin sun samar wa wasu 'yan kudaden jalli da shirya aiyukan raya karkara don karya lagon jama'ar da ke da dogon tsinkaye na zuwa ketare.

Magance matsalar kwadayin yin kaura tun daga tushe

Sai dai Saidou Abdou wani kwararre a fannin kaurar jama'a na mai cewar tallafin ne bai taka kara ya karya ba ta yadda zai sa 'yan kasar masu bukatar zuwa kasashen ketare su sauya tunani.

Ya ce: "Dan jarin da ake basu daga an yi kwanaki suka kare komawa suke tsohuwar hanyarsu. Ke nan mace-macen da ake samu a cikin teku zai sake dawowa a Nijar, sai kasar ta zama wata abar nuni, don abinda ke sa mutane su tafi, guda ne, matsaloli na rashin aiki da kwanciyar hankali da talauci. Wadannan abubuwan idan har ba tsayawa aka yi aka kawo masu magani ba ba ya yiwuwa duk wasu kwakkwaran matakan da za a dauka ba za su hana mutane tafiya ba."

Niger Ibrahim Yacouba

Ibrahim Yacouba: Nijar na neman maganin wannan bala'i

Lamarin dai na hasarar rayuka a Hamadar ta Saharar Nijar na zuwa a yayin da kasashen Turai ke shirin hada kai da wasu kasashe cikinsu har da Nijar don basu makudan kudin da zai sa su rinka dakile matsalolin na bakin haure tun daga gida. Duk kuma kokarin da aka yi domin jin ta bakin gwamnati haka ta kasa cimma ruwa. To amma a wata hirar da aka taba yi da tashar DW Ministan harkokin wajen Nijar Alhaji Ibrahim Yacouba ya ce kasar na cikin shirin neman maganin wannan masifa da ke neman ta samu gindin zama a arewacin kasar.

Jamhuriyar Nijar dai na bukatar CFA miliyan dubu 660 a wani jadawalin da ta wallafa wa hukumar EU a bara, kuma tuni kasashen suka fara agazawa da Euro miliyan 75 don dakile matsalar ta bakin haure da 'yan ci-rani.

Sauti da bidiyo akan labarin