Nijar: Mahawara kan makomar karatun boko | Siyasa | DW | 10.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Mahawara kan makomar karatun boko

A Jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta kira ministoci uku da ke a karkashin wani kwamitin da gwamnati ta kafa domin shawo kan matsalar karatu domin su bada ba'asi kan makomar karatun boko a kasar.

Tafiyar hawainiyar da karatun boko ke fuskanta a Nijar ta sanadiyar yaje-yajen aiki da malaman makaranta da ma dalubai ke yi, ya kawo babban nakasu a harkokin ilimi a wannan shekara. Kiyasi ya nunar cewa cikin watanni shida da kama karatu watani biyu ne kacal aka yi ana karatu, sannan kuma babu tabbatas dangane da ci gaban karatun a sauran watanni uku da suka rage kafin jarabawar karshen shekara, abun da ake ganin zai haifar da babban cikas ga sakamakon jarabawar da gwamnatin ta ce sai an yi ko ana ha-maza ha-mata.

Neman bakin zaran matsalolin ilimi a Nijar

Matsalolin dai da suka kawo tsaiko a karatun na bana sun hada rashin biyan malaman makarantu, da sauran cika wasu alkawura daga gwamnati a cewar maluman makarantar yayin da a hannu daya suma 'yan makaranta gami da dalibai na jami'a ke kokawa da rishin magance nasu matsalolin. 'Yar majalisa Hjiya Halima Mamman ta ce wasu makarantu da dama a cikin karkara na fuskantar karancin malamai, a yayin da a wasu makarantun na cikin birane ko manyan garuruwa ake samun cinkoson malumai. Sannan wata matsalar ita ce ta kai wasu maluman makarantar mata nesa da mazajensu.

Jijiyoyin wuya na tashi a harkokin bada ilimi

'Yan makaranta a Nijar na bukatar agaji

Wani batun kuma shi ne na takardun jabu da gwamnatin ta ce ta gano ga wasu malaman, hakan dai ya sansa gwamnatin ta Nijar daukan matakan bincike domin gano gaskiyar lamarin yayin kuma da ake tsakiyar shekara ta karadu har ma ana neman zuwa ga jarabawa. A cewar Ministan Dauda Mamadu Malam Marté da ke kula da kananan makarantu, wasu maluman da yawansu ya kai 997 da suka san basu da cikokun takardun sun yi layar zana yayin da masu bicike suka je a makarantun da suke koyarwa. Sannan kuma Minista Marte ya yi kira da a fitar da duk wata siyasa daga cikin harkokin karatu a kasar a dubi gaskiya, muddin dai ana son shayo kan matsalar da take neman zama gagara badau.

Sauti da bidiyo akan labarin