Nijar: Mahawara kan cigaba bayan samun mulkin kai | Siyasa | DW | 03.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Mahawara kan cigaba bayan samun mulkin kai

Masana da masu sharhi kan lamuran yau da kullum a Nijar na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan cigaba ko akasin haka bayan samun mulkin kai shekaru 55 da suka gaba.

Al'ummar Nijar da masana harkokin siyasa da na tattalin arziki irinsu Malam Sani Adamou na ganin ba zai yiwuwu ba a ce ba a samu cigaba a kasar ta fannin tattalin arziki da dimokradiyya ba shekaru 55 bayan da kasar ta samu ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa, duba da yadda lamura suka sauya daga lokacin da aka samu 'yancin kawo yanzu.

Öl Industrie Afrika Nigerianische Arbeiter der Akon Oil Company

Al'umar Nijar na kokawa kan rashin cin moriyar arzikin man fetur na kasar.

Malam Sani na da'awar cewa an samu cigaban ne a fannonin da suka hada da 'yancin fadin albarkacin baki da wayewar kan al'umma da sauran abubuwa da dama a cikin kasar, to sai dai wani bangare na al'umma na ganin cigaban fa bai taka kara ya karya ba. Malam Nsiri Sa'idu na daga cikin 'yan kasar da ke da wannan ra'ayi inda ya ke cewar cigaban mai hakar rijiya aka samu duba da irin sama da fadi da dukiyar kasar da kuma koma baya na tatatalin arziki da ake fuskanta.

Afrika Hungerkatastrophe Archivbild 2005

'Yan Nijar da dama na kokawa kan rashin kula da 'yan kasar.

Su kuwa wasu 'yan kasar da masu sanya idanu kan harkokin tattalin arzikinta na ganin an samu cigaba ta wannan fanni sai dai fa tattalin arzikin na makale hannun wasu 'yan tsiraru kana har ya zuwa yanzu abubuwa na more rayuwa ba su wadaci talakan kasar ba idan aka kwatanta hakan da yadda sauran jama'a suka a kasashe takwarorin Nijar din.

Al'ummar Nijar din dai yanzu haka na bege na ganin sun samu ingantaciyyar rayuwa inda talaka zai kasance cikin walwala da kuma kawo karshen rashin jituwa na 'yan siyasa wanda hakan mafi akasari kan jawo tsaiko wajen samun irin cigaban da ake zaton samu daga wadanda ke rike da madafun iko.

Sauti da bidiyo akan labarin