Nijar: Kyamar marayun kwayar cutar HIV | Zamantakewa | DW | 09.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Nijar: Kyamar marayun kwayar cutar HIV

A Damagaram na Jamhuriyar Nijar, yaran da iyayensu suka mutu sakamakon cutar AIDS ko Sida na fuskantar wariya daga al'umma, baya ga rashin samun tallafi daga kungiyoyin masu zaman kansu.


Kama daga iyaye maza da kuma mata da ke dauke da kwayoyin wannan cuta tun farkon bullarta, kyama na daga cikin abubuwan da ke ci gaba da sa su razanasu yaran musamman ma a bainar jama'a.


A cewar wata mata dai, a yanzu haka  'yan uwan miji ba sa kuma da da marayun diyan da mijinta ya bari, kan haka ne ma ta yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da su kawo musu dauki sakamakon matsanancin hali da suke ciki.


Wasu daga cikin marayun na Sida kira suka yi na a gaggauta kawo masu taimako ko sun dore da karatu. To amma a cewar shugaban kungiyar masu dauke da cutar ta sida shiyyar Damagaram matsalolin rashin samun taimakon sun dauko tushe tun daga zanga-zangar kin jinin jaridar Charlie Hebdo da ta yi zanen batanci ga shugaban halitta.