Nijar: Kalubale gabanin zaben 2021 | Siyasa | DW | 17.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Kalubale gabanin zaben 2021

Wasu jam’iyyun siyasar Nijar da suka hada MNRD Hankuri da RDR Canji sun kulla kawance tare da tabbatar da Alhaji Maman Ousmane tsohon shugaban kasar a matsayin dan takarar kawancen a zaben 2021

An dai gudanar da shagulgullan bukin kulla kawancen ne a yammacin jiya Lahadi tare da halartar bangarori daban daban na siyasar kasar da suka hada da yan adawa da da na bangaren masu mulki

Irin alkaryoyin da aka sha gudanarwa kenan a ya yinda jam'iyyun siyasar suka kaddamar da kulla kawancen mai suna ADR, wato Alliance Democratique et Republicaine da kuma ke shirin gudanar da gagarumar fafatuka irin ta siyasa wajen tunkarar kawancen jam'iyyun da ke mulki musamman ma PNDS Tarayya domin yin abinda suka kira kwatar goriba a hannun kutru.

Sai dai duk da yake kawancen ya jaddada matsayinsa na kasancewa a cikin gungun kawancen jam'iyyun da ke adawa na FRDDR mai jagorancin Hama Amadou, sabon kawancen ya zabi tsohon shugaban kasar Alhaji Mahaman Ousman a matsayin shugaba.

A yayin jawabinsa ya nuna matukar godiya ga daukacin jam'iyyun da suka damka masa wannan matsayi, tare kuma da nunabacin ransa dangane da halin da ya ce kasar ta ke a ciki a yanzu haka.

Sauti da bidiyo akan labarin