Kimanin kananan yara 24 sun mutu sakamkon tashin gobara a wata makaranta a Maradi da ke Jamhuriyar Nijar inda hukumomin gwamnati suka ce kusan dalibai 80 maza da mata sun samu raunika sakamakon konewa.
Gobarar ta tashi ne a azuzuwa uku da aka yi su da katakai a kudancin jihar Maradi, zuwa yanzu dai ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba.
Bangaren ilimi dai a Jamhuriyar Nijar ba ya samun kaso mai tsoka, matakin da ke da nasaba da rashin wadatattun makarantun boko masu inganci a kasar. Sai dai shugaban kasar na yanzu Mohamed Bazoum ya sha alwashin farfado da harkar ilimi a kasar.