Nijar: Ana taron inganta dimukuradiyya da mulki | Siyasa | DW | 01.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Ana taron inganta dimukuradiyya da mulki

Nijar ta karbi bakuncin babban zaman taron wata kungiyar farar hula ta kasa da kasa da ke sa ido wajen ganin ana gudanar da sahihiyar dimukuradiyya da mulki a cikin kasashen duniya.

Taron da shi ne irinsa na farko dai, za a kuma kwashi kwanaki biyar ana yin sa a birnin na Yamai, Kungiyar farar hula ta Tournons la page da ke nufin a buda sabon babi, kungiya ce da ke aiki a cikin kasashe guda takwas na Afirka da suka hada da Burundi, Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Chadi da Nijar da Togo da Kamaru da Senegal da kuma Faransa. Sai dai a wannan babban zaman taro na farko na kungiyar a birnin Yamai, an samu halartar karin wakillan wasu kasashe uku da suka hada da Cote d’voir da Gabon da Kwango Brazzaville da kuma Guinea.

A cewar shugabannin wannan kungiya dai ta Tournon la Page, shekaru biyar da suka shude, sun basu dabar samun karfi da kuzari, domin kuma duk wani kamu da aka yi wa daya daga cikin mamba, ko kuma furjin mussa da magabata ke yi musu duk abubuwa ne da ke kara musu kuzari na yin wannan kokuwa ta neman 'yancin ga Afirka.

Shugaban na kasa da kasa na kungiya ta Tournon la Page, ya yi tsokaci kan yadda kasashe da dama ke kaddamar da dokar takaita 'yancin fadar albarkacin baki ta yanar gizo, ko kuma katse internet a wasu kasashe, inda ya ce tafiyar na da nisa amma kuma lokaci ne na kowa ya zage dantse domin cimma buri kan yakar duk wani salo na kama karya a cikin harkokin tafiyar da mulki.

Sauti da bidiyo akan labarin