Nijar: An kammala yakin neman zabe | Labarai | DW | 20.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: An kammala yakin neman zabe

A cikin daren jiya Juma'a ce aka kawo karshen yakin neman zabe na shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da yi a gobe Lahadi.

Hankula al'ummar kasar dai yanzu haka ya karakata kan yadda wannan zabe zai gudana wanda shugaban kasar Mahamadou Isoufou zai fafata da 'yan takara 14 ciki kuwa har da Hama Amadou na jam'iyyar Moden Lumana Afirka wanda yanzu haka ke tsare a gidan kaso.

A bangaren 'yan majalisu kuwa, kimanin 'yan takara 5,200 ne daga jami'yyu daban-daban na kasar ke zawarcin kujeru 171 da ake da su a zauren majalisar dokokin kasar. Batun tsaro da dakile tashin hankali yayin zaben dai na daga cikin abubuwan da jami'an tsaro suka sanya a gaba a zaben na Nijar na bana.