Nijar: Amnesty ta soki tsare 'yan fararan hulla
May 26, 2018Akasari ana tsare da jagororin kungiyoyin fararan hullar na Nijar ne tun a watan Maris da ya gabata bayan wata zanga-zanga da hukumomin kasar suka haramta wadda kuma ta haifar da dauki ba dadi tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro.
Kungiyar ta Amnesty International da ta Oxfam gami da sauran gamayyar manyan kungiyoyi takwas masu zaman kansu na kasa da kasa, sun yi kira ga gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar da ta sassauta lamarin ta hanyar sakin dukannin mambobin kungiyoyin fararan hulla da take tsare da su, tare da kawo karshen matsin lambar da ake yi wa sauran abokansu a cewar sanarwar.
Wannan mawuyacin halin da kungiyoyin fararan hullan na Jamhuriyar Nijar suka shiga ya dauki hankalin manyan kungiyoyin na kasa da kasa masu rajin kare hakin jama'a da ma kungiyoyi na ci-gaba a cewar Adama Coulibaly Darektan kungiyar Oxfam na yankin yammcin Afirka.