1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ngozi Okonjo-Iweala za ta jagoranci kungiyar WTO

October 28, 2020

Manyan jakadu a kungiyar ciniki ta duniya WTO, sun gabatar da shawarar nada Ngozi Okonjo Iweala domin zama wacce za ta jagoranci kungiyar a nan gaba.

https://p.dw.com/p/3kXvD
Ngozi Okonjo-Iweala
Hoto: DW/U. Musa

Wannan mataki ya share mata fagen zama mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko, da za ta jagoranci kungiyar cinikin ta duniya tun kafuwarta shekaru 25 da suka gabata.

Koda yake shawarar jakadun na bukatar amincewar hukumar zartarwar kungiyar ta WTO, wannan shi ne matakin karshe na tsarin jadawalin zaben wanda zai cike gurbin da aka shafe watanni hudu ana yi.

Manyan jakadu uku da ake yi wa lakabi da Troika a turance a kungiyar ta WTO, waɗanda suka gabatar da shawarar zabar Ngozi Okonjo Iweala, sun yi hakan ne bayan shawarwari da kuma tuntubar wakilan kasashen kungiyar.

Ana sa ran samun amincewar ɗaukacin wakilan kasashe 164 na kungiyar cinikin ta WTO kafin tabbatar da nadin nata.