Nasarar kubutar da 'yan matan Dapchi
March 22, 2018Talla
Duk da cewar dai sun taru da sunan taron mako mako, tsallen murna ya mamaye fuskoki da bakunan 'yan majalisar zartarwar Tarrayar Najeriyar da suka karbi labari na sakin 'yan matan a cikin farin ciki.
Wata tattaunawar da gwamnatin kasar ta ce ta kunshi kungiyoyi na waje da ma abokai na gwamnatince dai a fadar ministan harkoki n labarai na kasar ta yi sanadiyar sakin 'yan matan.
Tun a farkon makon ne dai dama aka ruwaito ministan tsaron kasar Janar Mansur Dan Ali mai ritaya yana baiyana yiwuwar saki na 'yan matan da suka share tsawon wata guda a dokar daji suka kuma tilasta ziyara ta shugaban kasar ya zuwa kauyen Dapchin.