Buhari ya sha alwashin gano ′yan matan Dapchi | Siyasa | DW | 14.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari ya sha alwashin gano 'yan matan Dapchi

A bisa alamu na kulawa a rikicin satar 'yan mata 'yan makarantar Dapchi, shugaban tarrayar Najeriya Muhammadu Buhari ya share wunin Laraba yana ganawa da sarakuna da malaman addinai da sauran dattawa a jihar Yobe.

Sannu a hankali dai satar 'yan matan Dapchin ta fara daukar launi na siyasa, kuma sannu a hankali aka fara nuna alamun kasawa a bangare na gwamnatin tarrayar Najeriya da ke ikirarin cin nasara a yaki da Boko Haram amma ana jika.

To sai dai kuma Abujar na fatan sauya tunani tare da wata ziyara ta shugaban kasar domin jaje ga  daukacin al'ummar Yobe da iyayen yan matan Dapchin.

Kuma wani taro a tsakani na shugaban kasar da manyan sarakunan jihar da shugabanni na siyasa da malaman addinai da ragowar dattawan Yoben dai ya kare da tabbaci na shugaban kasar na gano dukkanin 'yan matan a cikin hali na lafiya:

"Zan iya bai wa iyayen yaran, da daukacin 'yan Najeriya da duniya tabbaci na yin komai a cikin karfinmu na dawo da 'yan matan  ga iyalansu a cikin hali na lafiya. Na bada umarnin a rika bani bayanai kullum kan  nasarori da kalubale na aikin ceto 'yan matan.  A yayin kuma da nake zaman jiran rahoton binciken satar 'yan matan, na umarci hukumomin da su hada  kai da jihar Yobe da ma makwabta na jihohi domin hada karfi da dabaru a cikin aikin ceton. Ba zamu sarara ba har sai mun tabbatar da ceto kowace yarinya ko dai ta Chibok ko kuma Dapchi."

An dai dauki lokaci ana musayar yawu a tsakanin jami'ai na 'yan sanda a jihar da rundunar sojoji ta kasar da ita kanta gwamnatin jiha game da inda laifi yake shiri ya baiyyana kan sakaci ko hada baki don satar 'yan matan.

Shi kansa shugaban dai ya sha alwashin daukar mataki na hukunci a wani abun da ke nuna alamun da biyu a cikin satar da wasu ke yiwa fassara irin ta siyasa , amma kuma  fadar kakaki na gwamnatin malam Garba Shehu sakamako na binciken ne kawai ke iya nunawa.

Abun jira a gani dai na zaman sauri na gwamnatin wajen nasarar ceto yan matan a cikin halin tattaunawar da gwamnatin ke yiwa kallo na fa'ida.

Sauti da bidiyo akan labarin