1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yaki da cutar zazzabin cizon sauro

April 25, 2024

Wani fitaccen malamin addinin Kirista a Najeriya, na fuskatar zargi a game da yada maganganu da ake ganin basu da asali a game da rigakafin cutuka musamman cutar zazzabin Malaria

https://p.dw.com/p/4fCAH
Malaria Mosquito
Hoto: James Gathany/AP/picture alliance

Malamin na Kirista wanda ya shahara a bangaren yada bishara, Chris Oyakhilome, ya sha yin maganganun da ke sanya shakku kan alluran rigakafi iri daban-daban a Najeriya a lokuta da dama da yake yi wa mabiya wa'azi. 

Sannannen malamin addinin Kiristan Christian Oyakhilome wanda ya fi shahara da suna Pastor Chris a takaice, ya jefa shakku a zukatan mutane lokacin wata hudubar da ya gabatar cikin watan Agustan bara inda ya zargi guda daga cikin manyan attajiran duniya Bill Gates da yin amfani da rigakafi da sunan taimaka wa kasashe matalauta a duniya, inda ya ce aikin da Bill Gates din ke yi ba komai ba ne face kokarin rage yawan al'umar duniya, attajirin da ya kasance guda daga cikin manya masu wannan aiki na taimako.

Karin Bayani: Za a fara allurar rigakafin zazzabin cizon sauro a Afirka

Mabiya addinin Kirista yayi taron Ibada a coci
Mabiya addinin Kirista yayi taron Ibada a cociHoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Shi dai Pastor Chris, shaharare ne sosai cikin masu bishara a nahiyar Afirka, to amma kuma mutane da dama na sukar maganganun da yake yadawa game alluran rigakafin.

Fitattun manyan kafofin watsa labarai na duniya sun bibiyi hudubobin da ya gabatar wa mabiya daga bara zuwa wannan shekara inda suka fahimci kwazon da yake nunawa wajen nuna lahanin da ke cikin rigakafi musamman na zazzabin cizon sauro da masana kimiyyar lafiya da magunguna a duniya suka samar a shekarar 2023 domin amfani da su a kasashen Afirka.

Cutar zazzabin Malaria dai babbar matsala ce da ta addabi al'uma matuka a Afirkar, inda kaso 95% na mace-macen da cutar ta haddasa a duniya a shekara ta 2022 suka kasance daga nahiyar.

Kare yara kanana daga cizon sauro
Kare yara kanana daga cizon sauroHoto: picture alliance/Photononstop

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kananan yara ne kaso 80 na wadanda cutar ke kashewa a duk shekara.

Amma, shi Pastor Chris malamin na Kirista mai karfin fada a ji ga al'umma mai yawa ya kai ga daukar mintuna 20 akalla, yana yada fatawar da ke adawa da rigakafin Malaria.

Fatawar kuwa, an yi ta ne cikin majami'a sannan kuma aka yada ta kai tsaye ta hanyoyin aika sako na zamani, abin da ya ci karo da tsari da hukunce-hukuncen kamfanonin da ke ba da wannan dama ta amfani da kafafen labarai, a game da yada farfaganda mara kan gado kan musamman magunguna na rigakafi.

Masana ilimin kimiyya dai sun kwashe gomman shekaru suna ta fadi tashin ganin sun samar da alluran rigakafin hana kamuwa da cutar zazzabin Malaria a duniya, kuma a karshe duniya ta yi murnar cimma nasarar samun hakan a bara tare da jinjina ganin dubban daruruwan rayukan kananan yara da za a iya cetowa daga ta'annatin wannan cuta.

Karin Bayani: Karuwar zazzabin cizon sauro a Najeriya

Allurar rigakafin Malaria
Allurar rigakafin MalariaHoto: Desire Danga Essigue/REUTERS

Tuni ma dai asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da nasarar aikin rigakafin cutar ta Malaria wanda aka fara a kasar Kenya da Ghana da kuma Malawi, aikin da ya samar da raguwar kashi 13% na mace-macen da malaria ke haddasa.

Kwararru a fannin lafiya a duniya na ganin wannan da'awa ta Pastor Chris Oyakhilome, ta yada maganganu kan rigakafin cutar na iya hana wasu yarda da maganin, inda suke fadin cewa lallai ne a maida hankali kan wannan abu da suka kwatanta da tabargaza.

A baya ma dai Pastor Chris wanda shi ne ya assasa majami'ar Christ Embassy, ya yi wasu fatawowi a kan rigakafin cutar sankarar mahaifa da kan sami mata.

Wannan kuma na zuwa ne yayin da Najeriya ta kaddamar da wani gangami na yi wa mata rigakafin sankarar mahaifa cikin watan Oktoban da ya gabata, kasar da a duk shekara, yara dubu ke rasuwa saboda cutar.

Haka kuma ya sha yin amfani da kalmomi masu adawa da rigakafin cutuka irin su tetanus da na shan inna, wadanda duk Bill Gates walau ya ke samarwa a kashin kansa ko kuma tare da hadaka da wasu manyan kamfanoni na duniya.