Najeriya:Cin hanci laifin shari′a ko zartarwa | Siyasa | DW | 12.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya:Cin hanci laifin shari'a ko zartarwa

A wani abun da ke zaman kokarinsu na wanke suna da kima a cikin nunin yatsa a bisa komawa bayan shari'ar cin hanci, babban alkalin Tarrayar Najeriya ya wanke alkalai.

An dai kira sunan alkalai an kuma ambato ramuwa irin ta gaiyar-gaiyya a cikin yakin shari'ar tarrayar Najeriyar da ya kalli koma baya sannan da barazana ta makoma sakamakon shari'u daga kotu da turjiya a bangaren 'yan doka.

To sai dai kuma daga dukkan alamu har ya zuwa  ga yanzu limaman yakin na cigaba a kokari na kaiwa ga gaci a cikin yakin mai tasiri.

Kama daga alkalan da ake zargi da juyin baya ya zuwa ga bangaren zartarwa da suke jagorantarsa dai, koma bayan da ya kalli asarar shiri'un dai ya gaza kaiwa ga dasushe kaifin yakin da ke kara nuna alamu na kwarjini a halin yanzu.

Ko a cikin wannan makonni dai hukumar EFCC mai jagorantar yakin ta yi nasarar bankado Naira  miliyan kusan dubu hudu a cikin wasu asusu guda biyu na banki a kasar.

To sai dai kuma su ma dai alkalai na kasar sun ce basu da niyya ta dakile yakin a fadar babban alkali na kasar da ya gana da shugaban kasar ya kuma ce a shirye suke domin hada kai da gwamnatin kasar domin nasarar yakin.

Mai shari'a Walter Onoghen da ya gana da shugaba Muhammadu Buhari cikin sirri dai ya ce alkalai a kasar ba su da sha'awa ta maida hannun agogo zuwa baya cikin yakin da ke yin sanyi yanzu..

Tuni  dai wani taron gaggawa na hukumomin yakar cin hancin a karkashi na mataimakin shugaban kasar da daukacin manya na hukumomin yakin hanci, da jami'ai a ma'aikatar shari'a ta kasar suka dauki  nazarin koma bayan da ke kama da halin alkalan amma kuma ke da launi na gazawa ta masu karar hancin.

Nazarin kuma da  Abujar ke fatan zai kai ga sake karfafa yakin da ke da tasiri ga kasar. Gwamnatin kasar dai ta ce ba ta da niyyar sauya shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu duk da bukata daga majalisar dattawa ta kasar.

Mallam Garba shehu dai na zaman kakaki na gwamnatin da ya ce hukuncin  alkalan da ma adawa daga majalisar ba su shirin rusa musu gwiwa cikin yakin da kasar ke da burin zai iya kaiwa ga bude sabon babi.

Sauti da bidiyo akan labarin