Najeriya:A hukunta barayin 'yan Chibok | Siyasa | DW | 19.08.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya:A hukunta barayin 'yan Chibok

Bayan mika wuya da wasu cikin wadanda suka sace 'yan mata 'yan makarantar sakandaren garin Chibok a Najeriya suka yi, wasu kungiyoyi na kira da a tabbatar an hukunta 'yan bindigar da suka yi sace su.

Nigeria 21 Chibok-Mädchen

Shekaru biyu bayan sace 'yan matan Chibok, wasu cikinsu sun kubuta

Shekaru bakwai kenan da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi awon gaba da 'yan matan daga makarantarsu da ke garin Chibok a jihar Borno. Kubutar biyu daga cikinsu dai, ta haifara da sabon fata bayan daukan dogon lokaci na fitar da rai a kan al'amarin nasu. 'Ya'yan kungiyar mayakanBoko Haram din dai, sun mika wuya tare da 'yan mata biyu wato Ruth da Hassana cikin wadanda suka yi garkuwa da su. 

Boko Haram na ci gaba da rike Leah Sharibu

Matakin mayakan dai, ya sanya kungiyoyi na yin kira da a hukunta wadanda suka sace su tare da yi musu auren dole, abin da Hosea Tsambido Abana na kungiyar BBOG ya ce kuskure ne ma a ce aurensu suka yi.

Ita ma kungiyar CSWN da ke nuna kawance, ta bukaci a tabbatar da nemawa 'yan matan adalci ta hanyar hukunta wadanda suka sace tare da yi wa 'yan matan auren dole, kamar yadda shugaban kungiyar Reuben Buhari ya bayyana cikin wata sanarwa. Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun 'yan bindigar na mika kansu ga sojojin Najeriya. A yayin da Najeriyar ke murna da wannan nasara ta mika kai da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi, masharhanta na ganin babban aiki a gaba shi ne na yafiya da karbarsu su zauna cikin al'umma domin wanzuwar zaman lafiya. Yafiya dai, na zaman muhimmin ginshiki a dukkanin manyan adinan Najeriyar biyu.

Sauti da bidiyo akan labarin