Najeriya: Ziyarar sakataren harkokin wajen Amirka | Siyasa | DW | 23.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Ziyarar sakataren harkokin wajen Amirka

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ke ziyara ta kwanaki biyu a kasar sun yi wata ganawa a fadar Aso Rock da ke Abuja.

A lokacin da ya isa fadar shugaban najeriya din, Kerry dai ya zarce kai tsaye ya zuwa tattaunawa da shugaban da ta share tsawon kusan sa'o'i biyu sannan kuma majiyoyi suka ce ta mai da hankali ga batun tsaro da yakin hanci na kasar. A baya dai gazawar Amirkan na saida makamai ga kasar ya kai ga jawo matsala a cikin dangantakar bayan da tsoffafin mahukuntan na Abuja suka zargi Washington da kin taimakawa yakin ta'addacin kasar a yayin kuma da Washington din ke cewar sojan kasar na da tarihin take hakkin dan Adam.

Ana dai kallon ziyarar da ake saran ita ce ta karshe ga wani jami'i na gwamnatin Obama da ke shirin barin gado a matsayin damar sake daidaita lamura tsakanin bangarorin biyu da ma kila samun agaji na kudi da makamai domin yaki da ta'addanci. Mr Geoffry Onyeama da ke zaman ministan harkokin wajen Najeriya ya ce Amurkan ta bayyana aniyarta ta biyan duk wata bukatar kasar ta fanni na tsaro.

Nigeria Boko Haram Terrorist

Amirka na kokarin taimakawa Najeriya wajen kawar da ta'addanci

Ga batun cin hanci kuma minista Onyeama ya ce suna goyon bayan duk abun da Najeriya ke ta wannan fannin, sannan kuma a nan ma sun bayyana aniyarsu na taimakon Najeriya kazalika sun ce suna shirin bada duk wata kafa da da za a iya amfani da ita domin karbo kudaden kasar da aka sace aka kuma boye su a Amirka. Tuni ma ministan harkokin shari'arsu ya shirya don bada wannan gudumawa kasancewar dama yaki da cin hanci na daya daga cikin abinda ya kware wajen yi.

To sai dai kuma ko bayan ganawa da shugaban kasar da Kerry ya yi, a share ya gana da wasu gwamnoni na arewacin kasar da suka hada da jihohin Borno da Adamawa da Bauchi da ke fama da matsala ta 'yan gudun hijirar Boko Haram. Amirkan dai na kallon mahukuntan kasar ta Najeriya a matsayin wadanda ake iya kaiwa ga amincewa a bisa imaninsu musamman ma bayan nasarar da gwamnatin kasar ta samu a cikin yakin na ta'addanci da kuma kokarin kai karshen halin berar da ke zaman ruwan dare a kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin