Najeriya: Zanga-zangar ′yan Shi′a a Abuja | Labarai | DW | 11.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Zanga-zangar 'yan Shi'a a Abuja

Jami'an tsaro a Abuja fadar gwamnatin Najeriya sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa 'yan kungiyar mabiya tafarkin Shi'a a wata arangama da suka yi dazu lokacin da 'yan Shi'a din ke wata zanga-zanga.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewar baya ga hayakin mai kwalla da aka harba, 'yan sanda sun yi harbi da bindigoginsu a kokarinsu na tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar wanda ke neman a saki jagoransu Sheikh Ibrahim el-Zakzaky.

Ya zuwa yanzu dai ba wani labari da aka samu na asarar rai ko jikkata sai da wanda suka shaida lamarin sun ce an kama wasu daga cikin 'yan kungiyar ta 'yan Shi'ar. 

Wannan dai na zuwa ne kwana biyu bayan wata arangama da aka yi da 'yan kungiyar da jami'an tsaro a harabar majalisar dokokin kasar inda suka je don neman majalisar ta sanya baki kan gwamnatin kasar ta sako shugabansu da ake tsare da shi duk kuwa da cewar kotu ta bada belinsa.