1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta shiga yarjejeniyar ciniki ta Afirka

July 12, 2018

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce zai sanya hannu kan yarjejeniyar ciniki ba tare da shinge ba a tsakanin kasashen nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/31IXw
Muhammadu Buhari
Hoto: DW/I. U. Jaalo

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce nan ba da jimawa ba zai sanya hannu kan yarjejeniyar nan ta ciniki ba tare da shinge ba, a tsakanin kasashen nahiyar Afirka.

Shugaban na Najeriya ya shaidar da hakan ne lokacin wani jawabin da ya yi wa manema labarai lokacin wata ganawar da ya yi da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, a birnin Abuja.

Cikin watan Maris da ya gabata ne dai kasashen Afirka 44 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, tare da kasar Afirka ta Kudu ta ita ma ta bi sahu a farkon wannan wata na Yuli.

Najeriyar dai ta bijire wa yarjejniyar cinikayyar da ta kai ta dala Tiriliyan uku tsakanin kasashen ne tun farko saboda kare harkokinta na arziki.  Sai dai daga bisani ta ba da uzurin bukatar nazartar lamarin da kyau tukuna.