Najeriya za ta kara wa′adin kawar da Boko Haram | Labarai | DW | 07.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya za ta kara wa'adin kawar da Boko Haram

Shugaba Buhari ya bayyana haka a cikin wani jawabinsa da Janar Abayomi Olonisakin ya karanta a wannan Litanin a gaban taron shugabannin sojin kasar da ya gudana a Jihar jigawa da ke a Arewacin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce wa'adin da aka dibar wa dakaran sojin kasar domin kawo karshen Kungiyar Boko Haram na iya zarce wanda aka tsaida tun farko.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a cikin wani jawabinsa da Janar Abayomi Olonisakin ya karanta a wannan Litanin a gaban taron shugabannin sojin kasar da ya gudana a cikin Jihar jigawa da ke Arewacin kasar.

Shugaban Buhari ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ya rage makonni uku wa'adin da ya bai wa sojojin kasar na su kawo karshen kungiyar ta Boko Haram ya cika.

Sai dai ya ce wa'adin ba wai kayyadadde ba ne, dama wata alama ce kawai , amma idan ta kama a sake tsawaita shi domin bai wa sojojin kasar damar fadada aikin nasu zuwa sauran jihohi , to kwa gwamnatin a shirye ta ke ta yi haka.

Duk da irin nasarar da sojojin Najeriya suka samu kan mayakan kungiyar a 'yan watannin baya-bayan nan, bai hana magoya bayanta ba su ci gaba da kai hare-hare a kasar ta Najeriya dama makobtanta.