Najeriya: Za a tuhumi Obasanjo kan kudin lantarki | BATUTUWA | DW | 23.05.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Za a tuhumi Obasanjo kan kudin lantarki

Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi a binciki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan badakalar kudi na dalar Amirka Miliyan dubu 16 da aka kebe don samarwa jama’a wuta lantarki a yayin mulkinsa.

 A baya sun hada kai da nufin tabbatar da kare mulkin ‘yan lema ta PDP a Najeriya, to amma kuma akwai alamar raba gari a tsakanin tsofaffin abokan takun guda biyu. Babu dai zato ba kuma tsamanni, shugaban da ke mulki  ya zargi  Obasanjo da watsar da tsabar kudi har dalar Amirka Miliyan dubu 16 amma kuma ba tare da yin tasiri a cikin masana'antar wutar kasar ba, lamarin da ya auku a lokacin da tsohon shugaban ke kan madafun iko.

Abun kuma da ya harzuka tsohon  shugaban da ya dora karatun jahilci ga Buharin tare da kalubalantarsa zuwa ga binciken batun. Ana dai kallon sabon rikici na abokan kuma duk tsofaffin janar janar na sojan a matsayin wani nau'i na siyasar da ake shirin gani cikin kasar anan gaba.

Tuni dai Obasanjon yai nisa a kokari na kare mulkin na Buhari tare da zaman babban jigo na masu adawar cikin kasar a halin yanzu. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin da ta kaya ga fage na siyasar dake niyyar tura daya a cikin tsofaffin janar janar na sojan ya zuwa gidan tarihi na siyasa.

 

Sauti da bidiyo akan labarin