Najeriya: ′Yan sanda sun ceto Ba′amirkiya | Labarai | DW | 13.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: 'Yan sanda sun ceto Ba'amirkiya

'Yan sanda a birnin Lagas a Najeriya sun yi nasarar kubutar da wata Ba'amirka wacce soyayyar facebook ta kai ta fadawa tarkon wani dan damfara da ya yi garkuwa da ita sama da shekara daya.

A Najeriya 'yan sanda sun yi nasarar kubutar da wata gyatuma Ba'amarika wacce soyayya ta kai ta ga fadawa hannu wani da ake zargin dan damfara ne wanda ya tsare ta sama da shekara daya ba da son ranta ba a wani otel na birnin Lagas.

Mutumin mai suna Chukwebuka Obiakuwhom ya hadu da matar ce 'yar asalin birnin Washington a soyayyar facebook wacce gyatuma ce da ta yi ritaya daga aiki inda ya yi mata alkawarin zai aurenta. Abin da ya ba ta kwarin gwiwar yin tafiyayya zuwa Najeriyar domin haduwa da masoyin nata inda ta iso a ranar 13 ga watan Feburairun 2019.

Amma zuwanta Najeriya ke da wuya sai mutumin ya kai ta wani Otel a birnin Lagas inda ya tsare ta ba da son ranta ba yana amfani da ita bayan ya karbe mata sama da Dalar Amirka dubu 48 da sunan zai aure ta a cewar hukumar 'yan sandan birnin na Lagas a wata sanarwa da ta fitar.