1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kuma sace dalibai a Kaduna

July 5, 2021

Sace mata masu-shayarwa da jarirai da wasu ma’aikata da 'yan bindiga suka yi a wani asibitin kutare da ke zaria ya kara jefa al'ummar jihar kaduna cikin rudani.

https://p.dw.com/p/3w3sW
Nigeria einige Schulkinder kehren heim | Katsina
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Zaria Entführungen.. - MP3-Stereo

Wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun kwashe dalibai a wata makaranta da ke yankin kudancin kaduna.

Da yammacin ranar lahadi wata kungiyar 'yan bindiga dauke da miyayun  makamai suka kai farmaki cibiyar kula da masu cutar kuturta da tarin fuka inda suka awon gaba da jarirai da kuma wasu ma'aikatan jinya.

'Yan bindigar sun kai hari ne garin saye inda cibiyar kula da kutaren ta ke da ke a wajen garin birnin zazzau inda suka fara bude wuta akan wani chaji offis din 'yan sanda. 

Akwai dai sabani kan yawan mutanen da 'yan bindigar suka yi awon gaba da su.

Sai dai tuni rundunanr ‘yan sandar kaduna ta tabbatar da aukuwar hadin inda kuma ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kamar dai yadda kakakin rundunar Mohammed Jalige ya saidawa manema labarai.