Najeriya: Yaki da cin hanci na ganin tasku | Labarai | DW | 06.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Yaki da cin hanci na ganin tasku

Wata kotu a Abuja fadar gwamnatin Najeriya ta wanke mai shari'a a babbar kotu Adeniyi Ademola da matarsa Tolulope Olabowale, da babban lauya Joe Agi.

A wani abu da ke nuna koma bayan da masu yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin Shugaba Buhari ke fuskanta a Najeriya, an janye tuhumar da ake wa mai shari'a Adeniyi Ademola  kan laifuka 18 ciki har da batun karbar cin hanci domin karkata hukuncin shari'a, inda masu gabatar da kara ke zargin an gano kudade Naira miliyan 30 a asusun matarsa da ba wa dansa mota kirar BMW.

Baya ga zargin gano kudaden kasashen waje da wasu bindogogi marasa lasisi a gidansa, ga zargin hannunsa da nuna son rai a shari'a da ta shafi wasu jiga-jigai a kasar kan batun Boko Haram da ma na 'yan fafutikar 'yancin Biafra wato Sambo Dasuki da Nnamdi Kanu.

Wannan dai na zuwa ne adaidai lokacin da babar kotu a Najeriyar a jiya Laraba a hukumance ta tuhumi Diezani Allison-Madueke tsohuwar Ministar man fetir a gwamnatin Jonathan da bada kudi Naira miliyan 264 ga wasu jami'an zabe uku kwana guda kafin zaben watan Maris na 2015.