1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yadda za a yi shari'ar 'yan Boko Haram

Salissou Boukari
September 29, 2017

Najeriya ta ce shari'ar mutanen da ake zargi da ayyukan Boko Haram da za a soma a ranar 9 ga watan Oktoba mai kamawa, za a yi ta ne cikin sirri ba tare da halartar dan jarida ba.

https://p.dw.com/p/2l038
Boko Haram Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo

An dai dauki wannan mataki ne bayan doguwar tattaunawa da aka yi tsakanin gwamnati da hukumar tattara bayannan sirri ta Najeriya DSS. Wani jami'in ma'aikatar shari'a ta Najeriya da bai so a bayyana sunn shi ba, ya ce akwai yiwuwar samun bayannai da za su iya kasancewa masu babban mahimmanci kan harkokin tsaron na Najeriya, wanda wallafa su ka iya kasancewa wani babban cikas a yunkurin da ake yi na samar da cikakken tsaro a kasar.

A makon da ya gabata ne dai ofishin ministan shari'ar na Najeriya ya sanar da cewa komai ya kankama wajen soma shari'ar mutane sama da 1600 da ake zargi da ayyukan Boko Haram, kuma za a yi shari'o'in ne a cibiyar sojoji na Kainji da ke jihar Kogi, da kuma ta New Bussa da ke Neja Delta, sannan da Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno inda Boko Haram din ta samo tushe.