1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zawarcin mukamin Abba kyari a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
April 20, 2020

A Najeriya an shiga kamun kafa na neman mukamin shugaban ma'aikata na fadar gwamnati, bayan rasuwar mutumin da ya yi suna da tasiri na karfin iko a wannan mukami wato marigayi Mallam Abba Kyari.

https://p.dw.com/p/3bBsA
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Tun kasa da sao'i 24 da rasuwar Mallam Abba Kyari ne dai, aka fara kamun kafa na neman wannan mukami da a yanzu ya tsole idanun mutanen da dama a Najeriyar. Kama daga 'yan siyasa zuwa 'yan boko har ma wadanda a zahiri mukamin da suke rike da shi a ya fi na shugaban ma'aikatan girma, sai dai kawai a yi batun tasirin da aka bashi a wannan gwamnatin. 

Tasirin iyayen gida

Tuni dai ake ambato sunayen mutanen da ake ganin 'yan cikin gida ne a fadar shugaban Najeriyar, wadanda ke takama ko dai da sanayya ko kuma iyayen gidan da suke shige musu gaba domin kai wa ga wannan matsayi.

Präsident Buhari steht dem FEC vor
Marigayi Malam Abba Kyari (na uku daga hagu)Hoto: Noso Isioro

Ga Barrister Mainasara Umar da yace mukamin aro shi Najeriya ta yi, ya ce kamata ya yi ayi wa mukamin na shugaban ma'aikatan gwamnati a fadar shugaban Najeriya garambawul.

Jiran tsammanin magajin Kyari

A yayin da ake ci gaba da kamun kafa na kai wa ga mukamin shugaban ma'aikatan gwamnatin a fadar shugaban Najeriyar, bisa la'akari da tasirin da yake da shi a yanzu, kallo ya koma sama inda ake jiran shugaban kasar Muhammadu Biuhari ya bayyana wanda zai gaji tsohon shugaban ma'aikatan gwamnati a fadarsa, da tunanin ko wanda za a nada zai yi tasiri ko akasi ga sauran shekarun da suka rage na gwamnatin mai ci yanzu.