Najeriya: Tashin hankali na yin illa ga samar da abinci | Siyasa | DW | 16.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Tashin hankali na yin illa ga samar da abinci

Tashin hankalin da wasu kasashen duniya ke fuskanta ciki kuwa har da Najeriya da ke fama da rikicin Boko Haram na daga cikin abubuwan da ke haifar da matsala wajen samar da abinci.

Mutanen garin Rann na jihar Borno da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Kamaru sun kasance masu dogara da noma domin samun kudaden shiga da kuma biyan bukatun su na yau da kullum sai dai duk lokacin da damuna ta shigo al'umma kan fuskanci tashin hakali saboda babu yadda abun hawa zai iya shiga ko fita wannan gari sakamakon rashin hanya.

Nigeria Maisfeld Bewässerung (DW)

Manoma ba sa iya noma gonakin da ke nesa da jama'a saboda fargabar hare-haren 'yan Boko Haram

Wata matsala har wa yau da ke barazana ga batun samar da abinci shi ne yadda al'ummar garin ba sa iya noma gonakin su manya sai kana da ke kusa da garin saboda yadda mayakan Boko Haram da ba su da nisa daga garin ke hallaka jama'a kamar yadda wani dattijo a garin mai suna Lawan Abacha Ibrahim ya shaida wa wakilin DW a Maiduguri Al-Amin Sulaiman Muhammad.

Wannan matsala dai ta sanya irin abincin da ake noma baya isar mutanen da ke wannan wajen kuma hakan na wakana ne daidai lokacin da aka samu 'yan gudun hijira daga wasu sassan jihar wanda suka gujewa rikicin Boko Haram. Wani mutum da wakilinmu ya zanta da shi ya ce wannan matsala ta kai ga sanya mutanen yin tsarin nan na musaya na ''ba ni gishiri in baka manda'' inda mai abinci ya bayar a bashi dabbobi ko wani abin bukata.

Nigeria Luftangriff auf Flüchtlingslager (Reuters/MSF)

Rikicin Boko ya sanya manoman garin Rann na jihar Bornon Najeriya yanke kauna da aikin gona

Yanzu haka dai jama'a na aza ayar tambaya kan mafita da ake da ita kan wannan hali na yunwa da al'umma suka samu kan su a ciki sakamakon gaza yin noma saboda matsalar tsaro. Duk da cewa wurare da yawa sun fara fitar da hatsi da suka noma a damunar bana amma lamarin ba haka ya ke ba a yankin Rann domin suna fara shuka dawar su ne bayan fara janyewar ruwa sama abinda ake ganin za a dauki lokaci kafin su fara samun saukin matsalar yunwa da su ke ciki.

Sauti da bidiyo akan labarin