1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sadarwa na samar da karin kudi ga Najeriya

November 28, 2016

A wani sabon haske da ake samu a batun tattali na arzikin Najeriya, harkokin sadarwa na neman maye gurbin man fetur a matsayin hanya mafi ba da agaji ga tattalin arzikin kasar da ke tangal-tangal.

https://p.dw.com/p/2TOn8
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Sai dai kuma sannu a hankali ragowar sassa na kasar na dada nuna alamar fatan sauyi ga kasar da ke cikin halin ni 'yasu da kuma ke neman mafita cikin ramar da ta yi mata sarkakiya. Na baya-baya a sabon fatan dai na fitowa ne daga harkar sardarwa inda a watanni uku na zango na uku na shekara mai karewa dai sadarwar ta kai ga tiriliyan daya da miliyan-dubu 400 na Naira ta kasar, ko kuma daya a cikin hudu na daukacin kasafin kudin kasar na shekara mai karewa. 

Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Ana dai kallon hobassar sadarwar da ta haura taimakon man fetur ga tattali na arzikin a watannin a matsayin wani abu da ke  iya taimakon Najeriya sake farfadowa daga suman da take yanzu. Wata sanarwar hukumar sadarwar kasar ta NCC dai ta ce sadarwar ta samar da kusan kaso daya da digo daya na karuwa ta tattali na arziki cikin kasar a  watannin Yuli zuwa Satumba.

Yawan masu amfani da yana ta gizo ya karu zuwa mutane miliyan 93 zuwa karshen watan Satumba na bana yayin kuma masu amfani da wayar salula suka kai milyan 153 a fadar sanarwar da ke dauke da sa hannun kakaki na hukumar sadarwar Tony Ojobo. Gwamnatin kasar tana kallon karuwar aiki da salular a cikin halin matsatsi da yawan kudaden da ke kasa na iya kaiwa ga sake dora dambar fata na fitowa a cikin rukukin a fadar Hajiya Zainab Shamsuna da ke zaman karamar ministar kasafin kudin, makuden kudaden da ake samu suna zamewa zuwa kasashe masu kamfanonin sadarwa da ke cikin kasar. 

Nigeria Abuja Benzinpreis
Hoto: picture-alliance/AA/Stringer

Har yanzu dai harkokin noma da ma'adinai na karkashin kasar da Abuja ke fatan za su maye hajjar man dai sun gaza tabuka komai duk da kaka mai kyawu da kasar ke takama da ita. Hasali ma dai Najeriyar ta ce tana shirin fuskantar matsalar yunwa sakamakon saye abinci zuwa ga makwabta a wani abun da ke zaman alamun sauran tafiya a kokarin kai wa ga tabbatar da noma ya zamo sana'a ta kan gaba da kasar ke iya zunkaho kanta wajen kudin shiga na kasashe na wajen ko bayan ci da kan da ba kwazo ba.