1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Najeriya na samun tallafi

Uwais Abubakar Idris LMJ
March 31, 2020

Kungiyoyin farar hula da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, sun nemi a sanya idanu kan kudin tallafin yaki da Coronavirus da ake tarawa domin kaucewa karkatar da su.

https://p.dw.com/p/3aH1g
Nigeria Politik l Senat
'Yan majalisun dokokin Najereiya sun bayar da tallafin CoronavirusHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Kiran kungiyoyin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tallafi na biliyoyin Naira daga 'yan Najeriya da kamfanoni da bankuna domin taimakawa gwamnati a yakin da take da annobar cutar Coronavirus, a yanayi da ken nuna hadin kai da yi wa matsalar taron dangi. Na baya-baya nan shi ne ministocin kasar da 'yan majalisar dattawa da suka bayar da rabin albashinsu. A nasu bangaren 'yan majalisar wakilan kasar sun bayar da albashinsu na watani biyu a matsayin tasu gudamawa.

#b#Duk da tallafin kudin da ake hasashen sun kama hanyar kai wa tiriliyan daya a  kasar baya ga alkawari na gina asibiti da attajirin nan Aliko Dangote ya yi a Kano, har kawo yanzu akwai jihohi da dama da babu na'urorin gwajin ga mutane da ma abin rufe baki da hanci da ke rage yaduwar cutar. Rashin cikakken bayani na adadin kudin da aka samu da inda aka ajiye su kuma me ake shirin yi da su ga alummar kasar, ya sanya  kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa cewa da sakel. A bayyane take cewa an yi wa cutar ta Coronavirus taron dangi, a yanzu ya rage na mahukunta su kamanta gaskiya da kuma bin ka'idoji ga 'yan Najeriyar na kyautata tsafta da bin dokoki na zama a gida a biranen da aka ayyana hakan.