Najeriya: Takaddama kan dokar zaben kasa | Siyasa | DW | 10.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Takaddama kan dokar zaben kasa

Wata takaddama ta kunno kai a game da kin sanya hannu da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a kan gyarar fuskar da aka yi wa dokar zaben kasar, bisa cewa yin hakan zai iya haifar da rudani a kan babban zaben 2019.

Bayan daukar dogon lokaci na mayar da dokar zaben ga ‘yan majalisar bisa abin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayyana da kura-kurai da ya kamata su gyara, a karshe ya ki sanya hannu a kan dukkanin gyare-gyaren da aka yi a kan dokar, ya na mai cewa sai dai ‘yan majalisar su ba shi tabbacin cewa ba za'a fara aiki da ita ba sai bayan zaben shekara mai zuwa na kasar.

Wannan ya harzuka mafi yawan jam'iyyun adawar Najeriyar da suke matsin lamba na lallai sai shugaban kasar ya rattaba hannu a dokar, saboda daukar lokaci da wahalhalun da aka yi a kanta. Ra'ayoyi sun sha bamban a tsakanin ‘yan majalisar na Najeriya a kan mayar da dokar da tun watan Febrairu suke aiki a kanta, kuma suke ganin su yi wa shugaban Najeriyar duk abin da ya ke so, don haka basu ga dalilin sake jan kafa a kan batun ba.

Sanata Ahmed Baba Kaita, dan kwamitin kula da harkokin zabe na majalisar ne ya ce shugaban na da ikon ya ki sanya hannu a kan dokar zaben, kuma dalilan da ya bayar ya kamata a yi la'akari da muhimmancinsu. A yayin da ake sa idon ganin mataki na gaba da majalisar za ta dauka, kwararru na bayyana samun daidaito a kan dokar zabe a matsayin muhimmin a dai dai lokacin da aka shiga jajibirin zaben da ya rage kasa da watani uku a gudanar da shi a Najeriyar.

Sauti da bidiyo akan labarin