1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Najeriya sun tsaurara tsaro a Abuja

October 28, 2022

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kara tsaurara tsaro a fadin kasar daidai lokacin da Amirka ta umurci ma'aikatan jakadancinta da zamansu bai zama dole a kasar ba su fice daga Abuja bisa yiwuwar kai hare-hare.

https://p.dw.com/p/4IoAl
'Yan sandan Najeriya cikin shirin ko-ta-kwanaHoto: Olamikan Gbemiga/AP Photo/picture alliance

Duk da cewa babu wani cikakken bayani kan gargadin da ofisoshin jakadancin wasu manyan kasashen duniya suka yi kan yiwuwar kai hare-hare, jama'a da dama a birnin Abuja sun shiga zullumi.

Sai dai a cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan kasar ta fitar ta ce ta umurci manyan jami'anta da ke fadin kasar da su kara kaimi wajen samar da tsaro musamman a birnin Abuja.