Najeriya ta sako mutane 128 da aka zarga da Boko Haram | Labarai | DW | 09.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta sako mutane 128 da aka zarga da Boko Haram

Hukumomin soji sun mika mutanen da suka hada da maza 109 da mata bakwai da kuma kananan yara 12 a hannu hukumomin Jihar Borno bayan da bincike ya wankesu .

Hukumomin sojin Najeriya sun saki wasu mutane 128 wadanda aka kama ake kuma tsare da su a bisa zarginsu da kansancewa 'ya'yan Kungiyar Boko haram. Tuni ma dai suka mika mutanan wadanda suka hada da maza 109 da mata bakwai da kuma kananan yara 12 a hannu hukumomin Jihar Borno.

A lokacin da yake jawabi a bikin sakin wadannan mutane shugaban hafsan sojin Najeriyar Janar Tukur Buratai ya ce sun kama wadannan mutane ne a makonnin baya a lokacin wani bincike da neman zagulo 'ya 'yan Kungiyar Boko Haram da suka gudanar a cikin Jihar ta Borno.

Kuma an sallamesu ne bayan da bincike ya wank su daga zargin da ake yi masu. Wannan mataki ya zo ne watanni biyu bayan da dama suka saki wasu mutanen 182 da suma binciken ya wankesu daga zargin kasancewa 'ya 'yan Kungiyar ta Boko Haram.