Najeriya ta janye matakinta kan asusun UNICEF | Labarai | DW | 15.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta janye matakinta kan asusun UNICEF

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da janye matakinta na haramta ayyukan asusun kula yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a yankin arewa maso gabashin kasar da ta sanar a ranar Juma'a.

Sojin Najeriyar dai sun zargi UNICEF din ne da horar da jami'an leken asiri, wadanda ke taimaka wa mayakan Boko Haram a kashe-kashen jama'a da suke yi a yankin.

A cewar rundunar cikin wannan makon asusun ya shirya wani taro a Maiduguri, inda ya horar da mutane, horon kuma da sojin suka ce zai donkofe aikinsu na yaki da ayyaukan 'yan tarzomar ta Boko Haram.

Sai dai bayan wata ganawa tsakanin sojojin da jami'an na agaji da yammacin Juma'a, rundunar ta sanar da janye matsayin saboda abin da ta kira shiga tsakani da aka yi.

Kwamandan runudnar yaki da ta'addanci a yankin, ya kuma gargadi UNICEF din da ta guji yin duk wani abin da ka iya shafar kokarinsu na murkushe rigimar da suke kai ba dare ba rana.