Najeriya ta yi kashedi ga 'yan jarida
January 8, 2019Ministan yada labarai na kasar ta Najeriya Lai Mohammed ne ya yi wannan gargadi a lokacin wata fira da 'yan jarida inda ya ce gwamnatin najeriya ba ta da nufin tauye 'yancin aikin jarida a kasar, amma kuma ya kamata a cikin aikin nasu kafafan yada labarai su iya rarrabewa tsakanin 'yancin fadar albarkacin baki da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su da kuma yada labaran da ka iya zamowa barazana ga tsaron lafiyar kasar.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai wasu sojoji da jami'an hukumar leken asirin cikin gida ta kasar suka kai samame a cibiyar jaridar Daily Trust a birnin Maiduguri inda suka tattare kayan aikin jaridar tare ma da iza keyar ma'aikatanta, biyo bayan wani labari da jaridar ta Dely Trust ta buga a shafinta na farko kan wasu bayanan sirri na sojojin kasar da suka hada da tasawirar shirin da sojin suka yi na neman karbo birnin Baga na yankin Tabkin Chadi daga hannun mayakan Boko Haram.