Najeriya ta ce ta sa kafar wando guda da Boko Haram | Siyasa | DW | 20.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta ce ta sa kafar wando guda da Boko Haram

Najeriya ta bi sahun makwabtanta wajen tinkarar Boko Haram, inda ta ce ta afkawa dajin Sambisa da ya dade da zama matattarar 'ya'yan kungiyar. Abinda ya sanya masharhanta bayani kan tasirinsa ga yaki da Boko Haram.

A lokutan baya an ta danganta dajin Sambisa da dodon da ya gagari sojojin Najeriya Shiga a yakin da suka kwashe shekaru shida suna yi da masu kai hare-hare. Sai dai kuma sannu a hankali sojojin Chadi da Kamaru da Nijar na samun nasarar karbo garuruwa da dama. Ita ma dai tarayyar Najeriya ta bi sahu inda ta yi ikirarin kai farmaki a wannan daji na jihar Borno.To shin me wannan ke nunawa a ikirarin da Najeriya ta yi na kawo karshen matsalar cikin makwani shida? Malam Kabiru Adamu masani ne a harkokin tsaro a yankin Afirka ta yamma.

'Na farko in har hakan ya kasance zai nuna cika alkawarin da shugaban kasa ya yi na cewa za'a kawo karshen lamarin cikin 'yan makwanni. Sai dai duk wanda ya ce zai kawar maka da ta'adanci cikin ‘yan kwanaki makaryaci ne, don ba zai yiwu ba cikin sati shida a kawar da wannan matsala. "

Maharba sun taimaka wajen yakar Boko Haram a Adamawa

Maharba sun taimaka wajen yakar Boko Haram a Adamawa

Kawar da fargaba da sojojin suka yi a yanzu na yin luguden wuta ta sama da ta kasa domin karya laggon wannan matsala ya sanya kallon lamarin ta hanyoyi mabambanta, musamman ganin yadda Najeriyar ke fuskantar zabe da kuma rashin tsaro da ya haifar da tsoro a zukatan al'umma. Shin me ya sa sai a yanzu ne sojoji suka afkawa Sambisa? Mike Omeri shi ne shugaban cibiyar samar da bayanai a kan harkokin ayyukan ta'adanci a Najeriya.

'Idan za'a je irin wannan yakin akwai irin tsarin da Majalisar Dinkin Duniya ta samar shi ya sa. Sojojin Najeriya a lokacin da suka yi yunkurin shiga wurin, an dasa nakiyoyi da sauran abubuwa, kuma suna neman kayan aiki da za su iya shiga. Yanzu sun samu kayan yakin da suke so shi ya sa suka bude wuta suka shiga."

Shugabannin Kamaru da Chadi da Nijar sun sa kafar wando daya da Boko haram

Shugabannin Kamaru da Chadi da Nijar sun sa kafar wando daya da Boko haram

Kwararru na bayyana tsoron tasirin da wannan shiri zai yi, sanin cewa sun dade da sakin jiki na gudanar da harkokinsu. Sannan 'yan Boko Haram sun kafa sansanoni ba a dajin Sambisa kadai ba, har ma da garuruwan da suka kame tare da kafa tuta. Shin wane kalubale ne ke a gaba a kan wannan lamari. Malam Kabiru Adamu masanin harkokin tsaro a yankin Afirka ta Yamma ya amsa wannan tambayar.

'Ga dukkan alama idan wannan hari da ake kai masu ya ci gaba, to za su koma kamar yadda suka fara watau sari ka noke. Abu ne mai yiwuwa mu ga sabbin hare-hare a wajen Borno da Adamawa . Idan aka kai masu hari a wuraren sauransu da ke waje za su kai hari a sauran wurare, don haka ba a bin mamaki bane a ga sabbin hare hare a wasu wurare, irin su Gombe da Bauchi har da Abuja da Kano da Kaduna.''

A yayin da sojojin kasashen Chadi da Jamhuriyar Nijar da Kamaru suke ci gaba da haduwa da Najeriya don yakar wannan matsala, ana cike da fatar ganin irin takun da wannan zai haifar musamman yadda ake fuskantar sabbin hare-hare a kasashen makwabta na Nijar da Kamaru inda a can baya basu fuskanci wannan matsala ba.

Sauti da bidiyo akan labarin