Najeriya ta bude filin jiragen saman Abuja | Labarai | DW | 18.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta bude filin jiragen saman Abuja

Gwamnatin Najeriya ta bude filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa da ke Abuja, wannan dai na zuwa ne bayan dakatar da zirga-zirgan jiragen na tsawon makonni shida dan sabunta titin saukar jirage.

An dai bude filin jirgin ne kwana guda kafin cikar wa'adin da aka deba dan kammala gyaran, inda jirgin saman kasar Habasha na Ethiopian Airlines ya zama na farko da ya fara sauka a yau Talata a filin jirin na Namdi Azikwe International Airport da ke Abuja.

Sai dai rufe filin jirgin na wuchin gadi ya janyo cece-kuce a fadin kasar ganin filin jirgin na cikin filayen jiragen sama mafi zirga-ziga a yammacin Afirka wanda masana ke ganin rashin sa ido a kan gyara ne ya haddasa matsalar wanda dakatar da shi na lokaci kadan na haifar da koma baya a harkokin tattalin arzikin Najeriya.