Najeriya ta bankado sayar da manta a hanata kudin | Labarai | DW | 31.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta bankado sayar da manta a hanata kudin

Ana dai sayar da albarkatun man fetir din na Najeriya da ke zama jigo na hanyar kudaden shigar kasar, sannan a sa kudin a aljihun wasu mutane.

Niger Buhari Issoufou

Muhammadu Buhari

Mahukunta a Najeriya sun bayyana cewa sun gano wasu takardu da ke nuna cewa a lokutan baya an yi cinikin albarkatun man fetir da wasu jami'an gwamnatin kasar suka yi mai makon kudi a zuba su a asusun gwamnati sai a karkatar da kudaden zuwa asusun wasu mutane. Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana haka a zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba.

"A kwai wasu bayanai inda albarkatun man fetir aka fitar da su ba bisa ka'ida ba sannan kudaden da aka samu ta wannan ciniki aka mayar da su cikin asusun ajiyar wasu mutane ba na gwamnati ba".

Shugaban dai bai bada bayanai ba kan suwaye wadanda ke da hannu kan wannan ciniki da ma inda aka tura kudaden. Yayin tattaunawar da 'yan jarida shugaba Buhari ya tabo fannoni da dama baya ga yaki da cin hanci da rashawa da matsalar tsaro da kasar ke fiskanta.