Najeriya ta amince da kananan matatun Mai | Labarai | DW | 04.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta amince da kananan matatun Mai

Fadar shugaban kasa a Najeriya, ta ce gwamnati za ta halalta kananan matatun mai na 'yan ganima a yankin Niger Delta da ke kudancin kasar, inda za a rika sayar masu da danyen mai cikin sauki don su rika tacewa.

A cewar gwamnatin Najeriyar za a fara hakan ne a karshen shekarar da ake ciki, kamar yadda shugabannin yankin na Niger Delta suka bukata. A ranar Litinin da ta gabata ne dai jagabannin yankin Niger Delta, suka yi barazanar janyewa daga tattaunawar sulhu da gwamnatin Najeriyar, muddin aka ki amince wa bukatunsu nan da ranar 1 da watan Nuwamba.

Yanzu dai gwamnatin za ta samarwa kowacce daga cikin jihohin yankin mai arzikin mai, kananan matatu biyu-biyu wadanda za su fara harkar tace man da su. Akwai ma tattaunawar da ake kai da manyan kamfanonin irinsu Shell da Chevron, don su kafa manyan cibiyoyinsu a yankin na Niger Delta.

Amincewa hakan dai, na daga cikin dabaru ne na maganta fashe bututun mai da ke faruwa a yankin da mazauna ke cewa ba sa samun amfanin arzikin da ke a yankin na su.