Najeriya: Sojoji sun fafata da Boko Haram a Borno | Labarai | DW | 26.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Sojoji sun fafata da Boko Haram a Borno

Sojojin Najeriya sun fatattaki mayakan Boko Haram a wani yunkurin kungiyar na kwace iko da garin Magumeri da ke jihar Borno a arewacin kasar.

An samu musayar wuta mai tsanani tsakanin sojojin Najeriya da 'yan kungiyar Boko Haram, kamin daga bisani sojojin suka yi nasarar korar mayakan da suka fantsama cikin jeji. 

Rahotannin farko na cewa mayakan sun kashe sojoji uku, amma wani mamba a kungiyar 'yan sa kai da ke taimaka wa sojoji yakar Boko Haram ya tabbatar wa kamfanin dillacin labarun Reuters cewa sojoji shida ne suka mutu, tare da 'yan kato da gora uku da wani farin hula guda.

Rundunar sojojin Najeriyar ta karyata ikirarin kungiyar na kwace garin Magumeri. Wannan hari dai shi ne hari na baya-bayan nan da kungiyar ta kaddamar a jihar Borno, tun bayan harin kunar bakin wake da ya kashe mutane akalla 50 a cikin masallaci a karamar hukumar Mubi da ke arewacin jihar Adamawa a farkon mako.