Rikicin ta'addanci ya lakume rayukan sojoji 100
January 18, 2019Talla
Rahoton ya kara da cewa, maharan da suka kai wadannan hare-haren, sun yi nasarar sace tarin makamai a yayin artabu da sojoji a yankin. Hare-hare a garuruwan Baga da Kawa a ranar 26 ga watan Disambar bara ne aka tafka asarar rayukan, inda rikicin ya kuma tilasta wa mutum sama da dubu shida tserewa daga gidajensu. An sami karuwar hare-hare na ta'addanci a makonnin da suka gabata inji rahoton.
Wani jami'in hukumar jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriyan Edward Kallon, ya ce aikin isar da kayayyakin agaji na fuskantar tsaiko a dalilin yawaitar hare-haren ta'addanci da ake ci gaba da samu. Musanman ga wadanda aka tsugunar a wani sansani da ke garin Rann na jihar Borno.