1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siemens zai samar da lantarki a Najeriya

July 22, 2019

 A ci gaba da kokarin neman mafita daga matsalar rashin lantarki a Najeriya, gwamnatin kasar da kamfanin Siemens na kasar Jamus sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta wutar lantarkin da ma kara yawanta a kasar.

https://p.dw.com/p/3MYZu
Afrikaische Stromversorgung
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo



Karkashin yarjejeniyar da ke biyo bayan wata ziyarar aiki ta shugabar gwamnatin Jamus a bara, kamfganin na Siemens na kasar ta Jamus zai taimaka wa kasar kara yawan wutar lantarkin zuwa Megawatt 7,000 nan da shekara biyu a yayin kuma da kasar za ta kai ga Megawatt dubu 11 a shekara ta 2023, sannan kuma ya zuwa megawatt  dubu 25 a nan gaba. Kamfanin dai zai samar da sabbabin na’urori da kuma inganta injina na samar da wutar Tarrayar Najeriyar da raba ta a fadar Shugaban Kamfanin Siemens din Joe Kaeser da ya rattaba hannu a madadi na kamfanin:


“Za mu tsara sabon shirin samar da wuta na Tarrayar Najeriya mai fuska uku a kashin farko za mu kara yawan wutar da ake samarwa zuwa Megawatt dubu bakwai, kashi na biyu zai kara yawanta zuwa Megawatt dubu 11 a yayin kuma da kashi na uku zai kai ta zuwa Megawatt dubu 25. Adadi ne mai girma kari ne mai tasirin gaske sannan kuma shi ne ake bukata domin dora kasar bisa turbar ci-gaba da mai da ta irin ta zamani”.

Siemens und Nigerias Regierung vereinbaren Plan zur Elektrifizierung
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Joe Kaeser babban darakta na kamfanin Siemens bayan sanya hannu kan yarjejeniyar inganta wutar lantarki a Najeriya.Hoto: New Media Unit, Presidency of Nigeria


Sabuwar yarjejeniyar dai na shirin diga dan bar samo hanyar warware matsalar wutar lantarkin da ke zaman karfen kafa cikin kasar na lokaci mai nisa. Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ana sa ran cin nasarar shirin wanda ya ce zai kara habbaka dama ta kasar cikin tsarin kasuwa guda maras shinge ta Afirka inda ya yi karin bayani yana mai cewa:


"Wannan tsari ba zai iya warware daukacin matsalolinmu cikin harkoki na wutar ba, amma dai ina da kwarin gwiwar zai kai karshen kalubalen da muke fuskanta na shekara da shekaru. Fatanmu shi ne in an samu ci-gaban wuta to kuwa za’a samu karin zuba jari, samar da ayyukan yi da kuma rage tsadar harkoki na kasuwanci a kasa da kuma kara habbaka tattali na arziki a Tarrayar Najeriya”

Siemens und Nigerias Regierung vereinbaren Plan zur Elektrifizierung
Babban Daraktan Kamfanin Siemens Joe Kaeser na gaisawa da Alex Okoh shugaban hukumar kula da huldar cinikayyar Najeriya da kamfanonin ketare a gaban Shugaba Buhari.Hoto: New Media Unit, Presidency of Nigeria


Yarjejeniyar dai na zaman biyo bayan ziyarar Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a watan Agustan bara inda 'yan kasuwar Jamus din suka nuna sha’awarsu ta zuba jari a cikin harkoki daban na kasar. Ambassada Yusuf Tuggar jakadan Tarrayar Najeriyar a kasar Jamus ya bayyana tasirin da wutar za ta yi ga rayuwar talaka a kasar. Shima Malam Usman Gur shugaban kamfanin rarraba wuta a Najeriya wato TCN na ganin shigar kamfanin na Siemens na nufin bude sabon babi a cikin masana’antar wutar kasar mai rikici.
Abin jira a gani dai na zaman iya kaiwa ga aiwatar da shirin da ke zaman na baya-bayan nan ga kasar d a baya ta sha rattaba hannu a cikin shirin gyaran wutar amma kuma shirin yana karewa a takarda.