1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyu 70 sun sa hannu a daftarin zaman lafiya

February 13, 2019

A cigaba da kokarin neman kau da barazanar tada hankalin da ke neman jawo matsala ga zabukan Najeriya, 'yan takara 70 sun rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar karbar sakamakon zaben.

https://p.dw.com/p/3DJcj
Vor Wahlen in Nigeria  Muhamadu Buhari (M), Präsident von Nigeria, und Atiku Abubakar (r)
Hoto: picture-alliance/AP/B. Curtis

A gaban manyan 'yan kallon cikin gida da ma waje ne dai manya da kanana na masu takara ta shugaban kasa suka rattaba hannu a bisa wata sabuwar yarjejen iyar dake zaman ta biyu cikin tsawon wata biyu.

Yarjejeniyar dai ta tanadi kaiwa ga gudanar da zabukan cikin zaman a lafiya da kuma karbar sakamako bayan tabbatar da shi.

Kuma kama daga shi kansa shugaban kasar ya zuwa ga madugun adawa ta kasar dai  daya bayan daya a cikin masu takarar sama da 70 suka rika rattaba hannun amincewa da yarjejeniyar da ke zaman gada a tsakanin kasar da fadawa rudani.

Akwai dai alamun dardar tun daga kalaman manyan jam'iyyun kasar guda biyu da kuma yadda magoya bayan jam'iyyun suka rika kai hari a kan abokai na hammaya a kwanakin dake gabatar zaben.